'Masu jihadi za su gama da Amurka'- Mutallab

Image caption Umar Farouk Abdulmutallab

Dan Najeriyan nan da ake zargi da yunkurin tada bam a wani jirgin saman Amurka a shekarar 2009, Umar Farouk Abdulmutallab ya sha alwashin cewa masu jihadi za su gama da kasar Amurka.

Umar Farouk Abdulmutallab ya bayyana hakan ne a lokacin da ake ci gaba da shari'ar da ake yi masa a wata kotu dake birnin Detroit a kasar Amurka

A ranar Kirsimetin shekara ta 2009 ne aka kama Umar Farouk Abdulmutallab a kan hanyarsa ta zuwa Detroit a Amurka, inda kuma aka zarge shi da yunkurin tayar da bam a jirgin.

Kamfanin dillacin labari na AFP ya ruwaito cewa a lokacin da aka shigo da shi cikin kotu kafin alkalin kotun ta shigo, yana ta ihun cewa 'Anwar na da rai', ya ce masu jihadi za su gama da kasar Amurka.

Kisan Al-Awlaqi

An dai kashe Anwar Al-Awlaqi na kungiyar Al-ka'ida ne kwanaki hudu da suka wuce da wani jirgin saman Amurka mai tuka kansa a kasar Yemen.

Jami'an hukumar leken asirin Amurkan dai sun sha nanata cewa Anwar Al-Awlaqi na da hannu a yunkurin tada bam din a jirgin saman Amurka a shekarar 2009.

Sun zargi Al-Awlaqi da tunzura Abdulmutallab bayan da suka hadu a kasar Yemen.

A zaman kotun na jiya, an zabi masu taya alkali yanke hukunci.

Umar Abdulmutallab dai ya nace cewa shi zai kare kansa, a yayinda ya ki amincewa da lauyoyin da kotun ta kebe masa.

A ranar goma sha daya ga wannan wata ne dai za'a fara shari'ar gadan-gadan kuma Umar Faruk Abdulmutallab na fuskantar hukuncin daurin rai-da-rai idan har aka same shi da laifi.