Shell: Bama haddasa fitina a yankin Niger Delta

Wata kungiya da ke sa ido akan harkokin Mai da Iskar gas mai suna Platform, wadda ke da hedkwatarta a London, ta zargi kamfanin Shell da hannu a aikace aikacen keta hakkokin bil-adama, ta hanyar biyan makudan kudade ga kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin Niger Delta.

Kungiyar ta ce, kamfanin Shell yana da hannu dumu-dumu a tashe tashen hankullan da suka faru a yankin Niger Deltar, tsakanin shekara ta dubu biyu zuwa dubu biyu da goma.

Rahoton da kungiyar ta Platform ta fitar yayi zargin cewar, kamfanin na Shell ya biya makudan kudade ga kungiyoyi masu tada kayar baya - lamarin da ya kara dagula rikicin - wanda a wani karon har ya kai ga lalata garin Rumuekpe, inda aka yi kiyasin mutane sittin sun rasa rayukansu.

Sai dai kuma kamfanin na Shell ya musanta hannu a zargin da ake masa. Inda ya ce sun dade da amsa cewar kudaden da muke biya kamar yadda doka ta tanada ga 'yan kwangiloli da kuma jarin da suke zubawa domin kyautata rayuwar jamaa a yankin Niger Delta, na iya haddasa rashin jituwa a cikin al'umomi ko kuma a tsakaninsu.