Rasha da China sun ki amincewa da kuduri a kan Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Kasashen Rasha da China sun hau kujeran naki a wani kuduri da aka gabatar a gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda zai yi Allah wadai, da amfani da karfin soji da gwamnatin Syria ke yi akan fararen hula.

Kudurin dai na barazanar daukar mataki ne akan Syria idan ba ta daina ci zarafin al'ummarta ba.

Kasashen Rasha da China sun hau kujeran naki akan kudirin da wasu kasashen Turai su ka marayawa baya, domin sukar gwamnatin Syria saboda yadda take amfani da karfin soji akan Fararen hula.

Kasashen Faransa da Jamus da Portugal da kuma Burtaniya ne su ka marawa kudirin baya inda suka nemi sassauci akan mataki da Majalisar za ta dauka indan gwamnatin Syria ba ta daina cin zarafin al'ummarta ba.

Kasashen dai sun cire batun kakabawa Syria takunkumi zuwa barazanar daukar mataki a kanta. Rasha dai ta ki amincewa ne da kudurin saboda barazanar da aka yi akan Syria a cikinta a yayinda ita ko China ta ce bai kamata ana tsoma baki a al'amuran cikin gida a Syria ba.

Amurka ta yi adawa

Jakadan Amurka Susan Rice ta zargi kasashen biyu da yin kafan angulu ga kudurin da zai kawo karshen cin zarafin fararen hula da ake yi a Syria inda ta ce, suna taimakawa gwamnatin na Syria ne wajen ci gaba da aikata ba dai-dai ba.

"Kasar Amurka na cikin kunci saboda yadda Majalisar ta gaggara magance matsalar tsaro cikin gaggawa a kasar ta Syria wanda kuma zai iya zama kalubale ga harkokin tsaro a yankin."

A lokacin da Jakadan Syria yake jawabi bayan an gama kada kuri'a akan kudurin, Jakada Rice ta fice gada Majalisar ne domin nuna adawarta.

Kasashen Rasha da China dai sun ce baza su goyi bayan wani kuduri akan Syria ba, saboda gujewa abun da ya faru a Libya.

Kasashen biyu dai sunce an zartar da kudurin kare fararen hula ne a Libya, amma sai aka yi amfani da damar wajen tunbuke Kanal Gaddafi daga kan Mulki.

A yanzu haka dai sama da watanni shida kenan da ake dauki ba dadi tsakanin masu zanga zanga da gwamnatin Syria, amma har yanzu kan membobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yaki ya haduwa waje guda domin an samu alkibla daya akan Syria.