Gwamnatin Bahrain na neman gyara sunanta

Masu Zanga zanga a Bahrain Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu Zanga zanga a Bahrain

Mai gabatar da kara na gwamnatin Bahrain Dr Ali Al-Boainain ya umarci da a sake shari'ar da aka yi wa wasu ma'aikatan lafiya 20 wadanda aka yanke musu hukuncin daurin da ya kama daga shekaru 5 zuwa 15.

Ana dai tihumar mutanan da taimakawa masu zanga-zangar adawa da gwamnati.

A makon da ya gabata ne wata kotun soji ta same su da laifin taimakawa wajen kifar da gwamnati, lokacin zanga-zangar sauyin da aka yi a watannin Fabreru da Maris.

Ya ce babu wani jami'in lafiya da za a ladabtar kan ya gudanar da aikinsa. Za asake shari'ar ne a kotun farar hula.

Wakiliyar BBC ta ce kasashen duniya sun yi Allah wadai da hukuncin na farko.

Da dama daga cikin ma'aikatan lafiyar sun ce an tilasta musu ne wajen amincewa da laifin da aka zargesu.