'Yan kwadago a Najeriya sun yi tir da shirin janye tallafin mai

Ngozi Okonjo-Iweala, Ministar Kudi ta Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ngozi Okonjo-Iweala, Ministar Kudi ta Najeriya

Kungiyar kwadagon Najeriya ta ce ba ta yarda da yunkurin gwamnatin kasar na janye tallafin da take bayarwa a bangaren man fetur ba.

Kungiyar ta kuma yi tir da shirin, kuma ta ce, za ta kalubalanci lamarin nan ba da dadewa ba.

Kungiyar na mai da martani ne ga fitowar da shugaban kasar ya yi ya bayyana aniyar janye tallafin.

Kungiyar kwadagon dai ta sha jaddada cewa za ta yi fito-na-fito da gwamnati idan ta janye tallafin.

Tuni dai wasu masana kan harkokin tattalin arziki a Najeriyar suke bayyana cewar, ya kamata a cire wannan tallafi domin kuwa babu wani taimako da yake yiwa talaka.