Red Cross ta fara aikin bayar da agaji a Somalia

Tambarin kungiyar Red Cross Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambarin kungiyar Red Cross

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta fara rarraba kayan abinci ga mutane fiye da miliyan daya wadanda mummunan karancin abinci ya shafa a Somalia -- a yankunan da kawo yanzu ba su samu wani taimakon kirki ba.

A karkashin wani shiri da zaa fara babu tsayawa, zaa dauki kayan abinci daga bakin gaba zuwa can cikin yankunan da ke hannun 'yan tawayen kungiyar Islamar nan ta Al-Shabaab.

Geoff Loane, wakilin kungiyar ta Red Cross a nan London, ya ce sun samu daidaitawa ne da kungiyar ta al-Shabaab domin kai wadannan kayan abinci.

Ya ce, "wannan shiri ne na tsawon watanni ukku, wanda a karkashinsa za rarrabawa mutane fiye da miliyan guda a kowane wata kayan abinci, shine burinmu, kuma an shirya ne musamman domin mutanen da ke yankunan da ke karkashin kungiyar Al-Shabaab."