BBC za ta rage ma'aikata dubu biyu

Mark Thompson
Image caption Darakta Janar na BBC Mark Thompson ne ya sanar da shirin

BBC na shirin rage ma'aikata 2,000 da sauya yadda take gudanar da shirye-shiryenta na talabijin domin rage kashi 20 na kasafin kudinta cikin shekaru biyar masu zuwa.

Babu wata tasha da za a rufe, amma za a yi amfani da wasu kudaden wajen shirya sababbin shirye-shirye.

Duka shirye-shiryen rana za su koma BBC One, yayin da BBC Two za ta rinka maimaita shirye-shiryen dare.

Darakta Janar na BBC Mark Thompson shi ya kaddamar da shirin wanda aka yi wa lakabi da gabatar da shirye-shirye masu inganci wato Delivering Quality First (DQF) a Turance - a wani jawabi da ya yi ga ma'aikata a ranar Alhamis.

Thompson ya ce "sauye-sauyen za su samar da wata sabuwar BBC wacce ke hade a wuri guda".

Baya ga rage ma'aikata 2,000 da za a yi a BBC baki daya cikin shekaru biyar masu zuwa, wasu karin 1,000 kuma za su tashi daga London zuwa Salford - ciki har da matakin mayar da BBC Three zuwa Salford a shekara ta 2016.

Wakilin BBC na fannin kafafen yada labarai Torin Douglas, ya ce, BBC ta ce wannan shi ne sauyi mafi girma da aka taba yi a tarihinta, za a sauya yadda - da kuma inda ake gudanar da ita.

Za ta rage kasafin kudinta da fan miliyan 670 a duk shekara.

'Suna durkusar da BBC'

Yawancin kudaden za a rage su ne ta hanyar inganta shirye-shirye - rage ma'aikata 2,000, ciki harda masu rike da manyan mukamai 300.

Babu wani bangare da za a rufe, amma za a rinka maimaita shirye-shirye da dama a BBC Two da Radio 3; da kuma rage kashi 15 cikin dari na kasafin kudin da ake warewa domin daukar nauyin wasu wasanni.

BBC One, wacce za a rage kasafin kudinta da kashi 3, za a rage wasu shirye-shiryen nishadantarwa da ta ke gabatarwa "wadanda ba su da wani tasiri sosai", a cewar Thompson.

Sai dai kungiyoyin kwadago sun mayar da martani cikin fushi ga batun rage ma'aikatan.

Sakatare Janar na kungiyar Bectu Gerry Morrissey, ya ce kamata ya yi "a kira matakin rusa shirye-shirye maimakon inganta su".

"Suna raba mutane da ayyukansu, sannan suna durkusar da BBC," a cewarsa.

Thompson ya ce ma'aikatan da ke cikin hadarin rasa ayyukansu za a iya sake "basu horo, ko a sake musu wurin aiki".