Ana kara kai dauki ga Bankunan Turai dake cikin matsala

Jose Manuel Barroso

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Jose Manuel Barroso, Shugaban Hukumar Turai

Shugaban hukumar tarayyar Turai, Jose Manuel Barroso, ya yi kira ga kasashen kungiyar da su dauki matakin karfafa bankunan turai domin kare su daga barazanar matsalar basukan da kasashen dake amfani da kudin Euro ke fuskanta.

Mr Barroso ya ce an nemi dukaN gwamnatocin kungiyar tarayyar turai da su kara zuba kudade a bankunan yankin domin karfafasu.

Ya ce, "za mu yi dukkan abin da ya dace domin tabbatar da cewa bankunan turai na yin yadda ya kamata wajen samar da basuka ga jama'a da 'yan kasuwa."

Gwamnatin Birtaniya ta bada sanarwar kara zuba dala biliyan dari da goma sha shidda a kamfanonin hada hadar kudade.