Ana taro tsakanin Najeriya da Nijar a Kebbi

Jami 'ai da kuma kwararru kan harkokin huldar kasa da kasa daga kasashen Najeriya da Nijar sun soma wani taron a garin Birnin kebbi dake Arewacin Najeriya.

Suna dai ci gaba ne da tattatuna batutuwan da suka shafi hulda tsakanin kasashen biyu.

Ana yin wannan taro ne karkashin inuwar Hukumar kula da hadin kai tsakanin kasashen na Najeriya da Nijar .

Zai duba yadda za'a soma zirga-zigar jiragen kasa ta kan iyaka tsakanin kasashen biyu da kuma maido da zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin su wadda aka dakatar