Tsohon shugaban Apple Steve Jobs ya mutu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Steve Jobs ya dade yana fama da cutar Cancer

Dimbin jamaa sun yi ta tura sakonnin nuna alhini da yabo a shafukan sada zumunta na Intanet, sakamakon mutuwar daya daga cikin mutanen da suka kirkiro kamfanin kamfuta na Apple, Steve Jobs.

A China kadai, mutane fiye da miliyan 50 ne suka aike da sakonnin ta'aziyya.

Mr Jobs na cikin manyan 'yan kasuwar da suka fi fice a duniya kuma shi ne ke da alhakin kawo sauyi a duniyar kimiyyar kere-kere ta hanyar na'urorin komfiyuta na Macintosh, da iPod, da iPad da kuma wayoyin salula na iPhone, kuma miliyoyin jama'a ne a duniya ke amfani da wadannan na'u'ori a kowacce rana.

Shugaba Obama ya ce, Mr Jobs ya canza rayuwar jama'a tare da canza alkiblar masana'antu da dama.

Mr Jobs dai ya rasu ne a California, bayan ya yi fama da cutar daji ko Cancer, yana da shekaru 56.