"Mun gaza kan harkar tsaro." In ji Karzai

Shugaban kasar Afghanistan, Hamid Karzai, ya ce gwamnatinsa da dakarun kasashen waje sun gaza samar da tsaro ga jama'ar Afghanistan.

Da yake magana da BBC shekaru goma bayan da aka kifar da gwamnatin Taliban, Mr Karzai ya ce harkar tsaro na daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta gaza.

Shugaba Karzai ya ce a ganinsa kamata ya yi ace tuntuni NATO, da Amurka da makwabtansu Pakistan sun maida hankali kan mafakar 'yan Taliban, amma ba ayi hakan ba, duk da tunatarwar da suka yi ta yi.

Tun da farko dai Janar Stanley McChrystal na Amurka ya ce wani abin haushin ma shi ne Amurka ta shiga yaki a Afghanistan da tunanin abu ne mai sauki.