Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Yaran da ake haifa da nakasa

Image caption Ana haifar yara da dama da nakasa

Cibiyar magance cututtuka da hana afkuwarsu ta Amurka ta fassara nakasa a matsayin sauyin fasali na wani sashin jiki.

Hakan dai na kara tabbata ne musamman idan aka kwatanta shi da yanda ainihin fasalin wannan sashe ya kamata a ce yake.

Kamar yadda cibiyar ta bayyana, ta ce nakasa wata matsala ce da ke faruwa tun a lokacin da yaro ke girma a cikin mahaifiyarsa, kuma mafi yawan matsalolin na faruwa ne a watanni ukun farkon ciki.

Binciken masana kimiyya ya bayyana cewa akwai wasu abubuwa da ake danganta su da janyo nakasar jarirai tun suna cikin uwa da suka hada da rikidar wasu kwayoyin halitta.

Ko lahani ga jaririn tun yana ciki, ko kuma ga mahaifa, ko haihuwar dake tattare da matsaloli, ko idan sinadaran jiki sun daina yin aikin da ya kamata da ma wasu matsaloli.

Tarihi ya nuna cewa gurbatar muhalli ya taimaka matuka wajen haihuwar yara da dama a duniya da nakasa iri daban daban.

A karshen shekarun 1980, gubar shara ta yi sanadiyyar haihuwar fiye da yara ashirin da basu da yatsu a Burtaniya.

Haka ma tun bayan kare yakin Vietnam a shekarun 1970 ya zuwa yanzu, an haifi yara fiye da dubu dari da hamsin da nakasa sakamakon gurbatar muhalli da wani sinadari mai guba da sojin Amurka suka yi amfani dashi a lokacin yakin Vietnam.

A garin Falluja dake kasar Iraqi ma, an haifi yara fiye da dubu daya da nakasa sakamakon dai guba itama da sojin Amurka suka yi amfani da ita a lokacin yakin Iraqi.