Salva Kiir zai kai ziyara birnin Khartoum

Sugaban kasar Sudan ta kudu, Salva Kiir
Bayanan hoto,

Sugaban kasar Sudan ta kudu, Salva Kiir

Shugaban kasar Sudan ta kudu, Salva Kiir, zai yi wata ganawa da jami'an Sudan yau a birnin Khartoum a ziyararsa ta farko tun bayanda kasarsa ta samu 'yancin kanta.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai ta yi tsami musamman ma a kan batutuwan da suka danganci tsaron iyaka da kuma raba kudaden shigar da ake samu daga mai.

A baya dai Salva Kiir mataimakin shugaban kasa ne a lokacin da ake da Sudan daya, kuma ya yi aiki ki ne tare da shugaba Omar al-Bahsir.

A yanzu haka dai zai koma kasar Jamhuriyar Sudan ne a matsayin shugaban tasa kasar.

Amma dai dangantaka tsakanin kasashen biyu dai ta yi tsami.

Dubban mutane ne dai aka raba da gidajensu, saboda fadan da ake yi a garuwan da ke kan iyake na kudancin Kordofan da kuma Blue Nile.

Har wa yau rikicin da ake yi akan iyakar yankin Abei wani abu ne da ke kawo tsaiko tsakanin kasashen biyu, amma maganar a yanzu haka tana gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Har yanzu dai ba'a cimma yarjejeniya ba tsakanin kasashen biyu kan yadda za'a rika raba kudaden shigan man fetur din kasar.

A yanzu haka dai yajejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen biyu kan ketara iyaka ya kara bada dan kwariwa gwiwa amma daule a samu gaggarumin sauyi kafin a samu wani ci gaba tsakanin kasashen biyu.