Kwamitin binciken kisan masu zangaga a Malawi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban kasar Malawi, Bingu wa Mutharika

Shugaban kasar Malawi, Bingu wa Mutharika, ya shaidawa BBC cewa zai kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa domin duba hargistin da ya faru a zanga zangar da aka gudanar a kasar a watan Yulin da ya gabata.

Kwamitin dai zai lallubo musababin artabun da aka yi tsakanin 'yan sanda da masu zanga zanga, inda akalla mutane goma sha tara su ka rasa rayukansu.

Har wa yau kwamitin zai binciki mutuwar wani dalibi mai fafutuka a watan da ya gabata.

Shugaba Bingu wa Mutharika na fuskantar matsin lamba ne tun bayan zanga zangar da aka gudanar a watan Yuli a ciki da wajen kasar.

Kasashen yamma sun juya baya

Kasar Amurka dai ta dakatar da kashe kudade a kan ayyukan more rayuwa da take aiwatarwa a kasar, saboda kisan da aka yiwa masu zanga zanga a kasar.

Gwamnatin Burtaniya ma har wa yau ta dakatar da tallafi da take baiwa kasar.

Saboda irin wadannan damuwa da kasar ta shiga ne, shugaban kasar ya bayyana kafuwar kwamitin binciken.

Ya shaidawa BBC cewa kasarsa na bukatar tallafi daga kasashen duniya, a yayinda ya nace cewa kasar na da kyakyar dangantaka da kasashen duniya.

Neman sasantawa

Ya kara da cewa ya tura wata tura wata tawaga mai kafin gaske zuwa kasar Burtaniya domin a warware duk wata matsala dake tsakanin kasashen biyu.

Kungiyoyin fararen hula masu fafutuka dai na sukar yadda gwamnatin kasar ke tafiyar da harkar tattalin arziki da kuma keta 'yan cin bil'adama.

Tun bayan zanga zangar da aka gudanar a watan Yuli, ana ci gaba da kai hare-hare a ofisoshi da kuma gidajen shuganin 'yan adawa abun da kuma har yanzu dai ba'a san mutanen da ke kai harin ba.

Mista Mutharika ya ce zai duba batun harin, kuma zai zauna a teburin tattauna da masu adawa da shi.