Babban Bankin Najeriya zai iya barin darajar Naira ta fadi

Image caption Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi

Babban Bankin Najeriya ya ce a shirye ya ke ya rage darajar Naira idan aka kwantata ta da dalar Amurka.

Wannan matakin dai ka iya haddasa hauhawar farashin kayayyaki, musamman ma kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje.

Babban bankin na Najeriya na la'akari ne da yadda tattalin arzikin duniya ke tafiya, kuma duk wani yunkuri na hana darajar Nairar faduwa bai yi nasara ba.

Najeriya ta ce a shirye take ta bar darajar naira ta fadi warwas idan aka kwatanta da dalan Amurka, Idan har farashin danyen mai a kasashen waje ya ci gaba da faduwa, a yayinda kuma kokarin Bankin na daukaka darajar kudin kasar na ci tura.

Baban Bankin Najeriya dai na sanya hannunsa ne a kasuwar musayar kudaden kasashen waje, inda yake sayar da dala, saboda kada dala daya ta wuce naira dari da hamsin.

Har wa yau tsarin da bankin ya bi, bai yi tasiri ba, saboda asusun kudaden kasashen wajen kasar na nema ya kare saboda tsarin.

Babban bankin Najeriyar dai ya yi kokarin kare darajar Naira idan aka kwatanta da dala, a wani yunkuri kare tattalin arzikin kasar daga hauhawar farashin kayyayaki.

Wani tsarin kuma da Bankin zai iya amfani da shi domin rage hauhuwar farashi shine, na kara kudaden ruwa, amma masana na ganin hakan na iya shafar 'yan kasuwa da sauran jama'ar kasar masu aron kudi daga bankuna, abun da kuma ke iya dakushe ci gaba tattalin arzikin kasar.

Kasashen duniya da dama ne dai sukayi koyi da kin yaki da darajar kudadensu na tsawon lokaci, musamman ma idan aka yi la'akarin cewa Asusun bada lamuni na duniya ne ke baiwa masu sanya hannun jari shawara, kuma asusun na ganin ana baiwa naira darajar da ba ta kamata ba.

Idan har darajar kudin Najeriya ta fadi warwas idan aka kwatanta da dalan Amurka, kayayyakin da ake yi a kasashen waje za su kara tsada, wannan al'amari kuma zai sanya kayayyakin da Najeriya ke fitarwa kasashen waje kamar kasar Amurka su kara araha.