Mata uku za su raba kyautar Nobel ta zaman lafiya

Mata uku za su raba kyautar Novel ta zaman lafiya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kungiyar Amnesty International ta yaba da gwagwarmayar matan

A bana mata 3 ne cikin har da shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf za su raba kyautar lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya dangane da aikinsu a kan 'yancin mata.

Sauran matan sun hada da Leymah Gbowee mai fafutukar mata a Liberia da kuma wata mai fafutuka kan mulkin Demokuradiya daga Yemen, Tawakkul Karman.

Shugaba Liberia, Ellen Johnson Sirleaf ba boyayyiyar mace ba ce, kasancewar ita ce mace ta farko da ta zama shugabar wata kasa a Afrika.

Tana yawan gabatar da jawabai a zauren Majalisar Dinkin Duniya, da ma tarukan da kungiyoyin mata na duniya ke gudanarwa.

Sai dai ita kanta tasha fadin cewa bata manta da asalinta ba, wato tana tare da jama'arta wadanda akasarinsu manoma ne, da kuma 'yan tireda na kasar.

Ita kuma Laymah Gbowee, bata yi fice a wajen Laberiya sosai ba.

'Nuna amincewa da rawar da mata suka taka'

Amma a cikin kasar sananniya ce, domin a lokacin da aka yi yakin basasar kasar, ta jagoranci addu'o'in samun zaman lafiya.

Ms Gbowee wacce har ila yau ta shirya wata kungiyar mata da ta yaki 'yan yakin sa kai a Liberia.

Ta kuma ce kyautar wata manuniya ce ta irin rawar da mata suka taka wajen samar da zaman lafiya duniya:

"Ina ganin an bani kyautar ne tare da sauran matan biyu saboda ana ci gaba da nuna amincewa da rawar da mata suka taka, dama wacce suke ci gaba da takawa wajen sauya yadda al'ummarsu ke rayuwa, da ma sauran jama'a baki daya".

'Na yi farin ciki matuka'

Anata bangaren Tawakkul Karman, mai fafutukar ganin an tabbatar da tsarin dimokuradiyya a yankin kasashen Larabawa.

Ta yi fice wajen shirya zanga-zangar adawa da gwamnati a kasar Yemen, ta kuma bayyana kyautar tata da cewa wani tabbaci ne na cewa zaman lafiya ya yi nasara kan tashin hankali.

"Na yi farin ciki matuka da wannan kyautar, kuma na yi imanin cewa kyauta ce ga baki dayan 'yan kasar Yemen, matasansu da matansu, kai harma da matasa a kasashen Tunisia da Masar da Syria da kuma Libya".

Kungiyoyin mata da ma na kare hakkin bil'adama, ciki har da Amnesty International sun yi maraba da kyautar da aka baiwa matan.

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International, ta yi marhabin da shawarar kwamitin bayar da kyautar Nobel din tana mai cewar ta aminta da aikin masu fafutukar don kare 'yancin mata a duniya baki daya.