Ana shirin karbe garin Sirte baki daya

Hari a kan Sirte Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hari a kan Sirte

Dakarun gwamnatin wucin gadi a Libya sun kaddamar da wani kasaitaccen hari a kan Sirte tare da aniyar karbe garin daga sauran masu biyayya ga Kanar Gaddafi a can.

Harin ya soma tare da ruwan harsasan bindigogin atilere ba kakkautawa sannan kuma daruruwan mayaka sun soma dannawa zuwa tsakiyar garin.

Tuni dai fararan hula da dama suka fice daga garin, amma kokarin sasantawa da mutanan dake kare garin ya faskara.