Kasashen duniya sun yi Allah-wadai da kisan Meshaal Tamo

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption masu zanga zanga a Syria

Kasashen duniya sun yi Allah-wadai da kisan wani fitaccen jagoran 'yan adawa dan kabilar Kurdawa da wasu 'yan bindiga wadanda suka rufe fuskokinsu suka yi a Syria.

Faransa ta ce kisan Meshaal Tamo ya girgiza ta.

Har yanzu dai ba a fayyace ko su wanene 'yan bindigar ba, amma Amurka ta ce kisan ya nuna cewa Shugaba Assad yana nema ya kai kasar ya baro.

Wani mai magana da yawun fadar gwamnati ta White House ya yi kira ga Mista Assad ya sauka daga kan mulki.