New Zeland na fuskantar bala'in malalar mai

Malalar mai
Image caption Wuraren shakatawa na bakin ruwa a kasar New Zealand na fsukantar hatsarin gurbacewa sakamakon man dake malala daga wani jirgin ruwan daya lalace cikin teku

Ma'aikatan agaji a kasar New Zealand sun kaddamar da wani yunkuri na kwashe kimanin tan dubu biyu na mai a wani jirgin ruwan daya lalace a gabar tekun kasar.

An dai yi ta fargabar cewa mai yiwuwa jirgin ruwan mai suna Rena, ka iya fashewa sakamakon iska mai karfin gaske da aka yi hasashen zata abku a kasar a gobe litini.

Jirgin ruwan dai yayi ta zubar da mai ne tun bayan daya lalace a ranar laraba, kuma tuni wasu jiragen sojojin ruwan kasar har guda hudu suka isa wurin don taimakawa wajen kwashe man.

Fira Ministan kasar John Key wanda zai ziyarci wurin da jirgin ruwan ya lalace, ya bayyana cewa ana fuskantar hadarin gurbacewar wasu muhimman wuraren shakatawa dake bakin ruwa sakamakon man dake ta tsiyaya.