Sudan da Sudan ta Kudu na son zaman lafiya

Salva Kiir da Omar al-Bashir

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Salva Kiir da Omar al-Bashir

Gwamnatin Sudan a birnin Khartoum ta tsayar da wani wa'adi na warware takaddamar dake tsakaninsu da kasar Sudan ta Kudu.

Shugaba Umar al-Bashir ya ce, ya bada wa'adi ga kwamitoci daban daban, na su dauki matakan warware matsalolin.

Shugaban ya ba da sanarwar hakan ne, a lokacin wani taron manema labaru na hadin gwiwa da shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir, wanda ya kai ziyararsa ta farko a Khartoum, tun bayan samun 'yancin kasarsa cikin watan Yuli.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta ki kyautatuwa ne, a sakamakon batutuwan da suke takaddama kansu, wadanda suka hada da raba arzikin man petur, da kuma rikicin kan iyaka.