Za a binciki tarzomar da ta afku a Masar

Masar
Image caption Akalla mutane 25 ne suka mutu a tarzomar

Majalisar mulkin soji ta kasar Masar ta nemi a gudanar da binciken gaggawa kan tarzomar da ta barke tsakanin Kiristoci Kibdawa da kuma jami'an tsaro ranar Lahadi.

Majalisar ta gudanar da wani taron gaggawa a daidai lokacin da ake shirin yin jana'izar mutane 24 da suka mutu a tarzomar.

Tarzoma ta barke ne bayan wata zanga-zanga sakamakon wani hari da aka kai kan wata Majami'a a Aswan.

Ana ganin martanin da sojoji suka mayar ya kara rura wutar tarzomar - wacce ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 25 tare da jikkata wasu 300.

Irin wadannan tashe-tashen hankula dai na karuwa a 'yan kwanakin nan a kasar ta Masar.

Kibdawan wadanda adadinsu ya kai kashi 10 cikin dari na al'umar kasar miliyan 80 - na zargin hukumomin sojin da kasa basu kariya.

Wakiliyar BBC Yolande Knell a birnin Alkahira ta ce akwai matsin lamba kan jami'an gwamnati na su tabbatar da hadin kan kasar.

An tsaurara matakan tsaro

Jami'an sojin sun nemi gwamnati da ta gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin lamarin da kuma hukunta wadanda ke da hannu a ciki.

A wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar, sojojin sun ce za su dauki dukkan matakn da suka da ce domin tabbatar da tsaro, kuma a shirye suke su mayar da mulki ga hannun farar hula.

An tsaurara matakan tsaro a muhimman wurare a birnin Alkahira, tare da karin soji a ginin Majalisar dokoki domin kawar da duk wata barazana.

An kuma girke 'yan sanda a wajen asibitin Kibdawa, inda aka garzaya da yawancin wadanda suka mutu da kuma jikkata a tarzomar.

Wannan dai ita ce tarzoma mafi muni da ta afku a kasar tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak a watan Fabrerun bana.

Karin bayani