Obama ya nuna damuwa game da rikicin Masar

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama, ya ce ya yi matukar damuwa da mutuwar akalla mutane ashirin da hudu a rikicin da ya barke tsakanin mabiya addinin Kirista qib-d'awa da jami'an tsaro a Masar.

Wata sanarwa da ta fito daga fadar White House ta yi kiran da a ba mabiya kirista qib-d'awan kariya, ta kuma jaddada bukatar gudanar da zabuka a watan Nuwamba kamar yadda aka shirya.

Majalisar sojin kasar Masar ta umarci ministocin gwamnati da su hanzarta gudanar da bincike game da rikicin.

Shubagannin cocin Koptic sun dora alhakin iza wutar rikicin kan wadanda suka kira munafikai da suka shigo cikinsu.

Mabiya addinin kirista da ba su da rinjaye a Masar sun zargi jami'an tsaro da rashin ba su kariyar da ta dace.