Jami'an tsaro sun bude wuta akan masu hakar ma'adinai a Indonesia

Shugaban Indonesia
Image caption An kashe daya daga cikin masu aikin hako ma'adinai a lokacin wata zanga zanga da suka gudanar a wurin hakar ma'adinan zinari da copper na Freeport-McMoran a Grasberg

Wani shugaban kungiyar ma'aikata a kasar Indonesia ya ce jami'an tsaro sun bude wuta akan wasu ma'aikata dake yajin aiki a wani wurin hakar ma'adinai dake gabashin lardin Papua.

An dai kashe daya daga cikin ma'aikatan lokacin da suka gudanar da zanga zanga a wurin hakar ma'adinan zinari da copper na Freeport-Mc Moran a Grasberg.

'Yan kungiyar kwadagon sun ce an yi harbin ne bayan da ma'aikatan suka yi kokarin hana mutumin daya mallaki wurin hakar ma'adinan amfani da wasu ma'aikatan da aka sauya musu aiki.

Kimanin ma'aikata dubu goma ne dai suka shiga yajin aikin inda suke neman da a rubanya albashin su da kusan shida akan dala uku a kowane sa'a daya da ake biyansu yanzu.