Johnson-Sirleaf ke gaba a zaben Liberia

Ellen Johnson-Sirleaf Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabar Liberiya, Elen Johnson-Sirleaf.

Sakamakon farko na zaben shugaban kasa a Liberia ya nuna shugaba mai ci yanzu, Ellen Johnson Sierlieaf, ta samu rata mai yawa a kan abokin takarta mafi karfi, sai dai yawan bai kai na samun nasara kai tsaye ba.

Ellen John Sirleaf, wadda ke neman wa'adi na biyu bayan kwashe shekara shidda tana mulki, ta samu rata a kan babban abokin takararta, Winston Tubman.

Hukumar zabe ta ce shugabar ta samu fiye da kashi arba'in cikin dari na kuri'un da aka jefa, idan an kwatanta da shi Winston Tubman, tsohon jami'in difilomasiya.

Sai dai kuri'un da aka kirga zuwa yanzu ba su da yawa sosai.

Idan babu dan takarar da ya sami cikakken rinjaye sai an je zagaye na biyu ke nan.