An yi zabe lafiya a Liberia

Masu zabe a Liberia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zabe a Liberia

Rahotanni daga Liberia sun ce an rufe runfunan zabe bayan zaben shugaban kasar na biyu tun karashe yakin basasar kasar shekaru 10 da suka wuce.

Rahotanni sun nuna cewar an yi zaben lami lafiya, kuma mutane da yawa ne suka fita kada kuri'unsu.

Tun kafin asubahi ne dai mutane suka kafa dogayen layuka duk kuwa da ruwan saman da aka tabka.

Duka manyan yan takarar shugaban kasar biyu, watau shugaba mai ci, Ellen Johnson Sirleaf da kuma tsohon jakadan Liberia a MDD, Winston Tubman, sun ce sun gamsu da yadda aka gudanar da zaben.