'Mai yiwuwa a samu juyin-juya hali a Najeriya'

Mai yiwuwa a samu juyin-juya hali a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin ya haifar da asarar rayuka da dama

Mai yiwuwa a samu juyin-juya hali a Najeriya matukar ba a dauki matakan inganta al'amura ba, a cewar kwamitin da gwamnatin kasar ta kafa domin duba musabbabin rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa na 2011.

"Tsananin bukatar neman sauyi da damuwa da jama'a ke nunawa kan gwamnatocin da suka gabata na kasa tallafawa rayuwarsu, su ne musabbabin tashin hankalin," a cewar rahoton kwamitin binciken.

Shugaban kwamitin Dr Sheik Lemu shi ne ya jagoranci gabatar da sakamakon binciken ga shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan.

"Rashin tsaron lafiya da dukiyar jama'a da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa sun kara fusata jama'a.

"Babu shakka wannan ka iya kaiwa ga juyin-juya hali idan ba a dauki matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar ba," a cewar kwamitin.

Kwamitin ya kara da cewa irin zanga-zangar da ake fuskanta a makarantun gaba da sakandare da na kungiyoyin kwadago, alamu ne na irin munanan abubuwan da ka iya fuskantar kasar a nan gaba.

Wani abu da kwamitin ya bayyana da cewa na da nasaba da rikicin, shi ne yadda 'yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati ke gabatar da bukatun kawunansu maimakon na jama'a.

Yawan kafa kwamitoci

Wakilin BBC Ibrahim Isa a Abuja, ya ce batun kafa kwamiti da kuma karbar rahoton bincike ba bakon abu ba ne a kasar - sai dai ba a fiye aiwatar da rahotonnin kwamitocin ba.

Image caption Rikicin ya kuma raba wasu daruruwan mutane da gidajensu

Wakilin na mu ya kara da cewa akwai rahotannin kwamitoci da dama da ke gaban gwamnatin, wadanda suka hada da na rikicin Boko Haram, Jos da Bauchi da makamantansu - wadanda kawo yanzu ba a aiwatar da su ba.

Shi ma kwamitin na Lemu ya nemi gwamnatin da ta aiwatar da sakamakon binciken wadancan kwamitoci da kuma hukunta wadanda ke da hannu kan lamuran da suka faru.

Har ila yau kwamitin ya ce jama'ar da ya tattauna da su sun nuna damuwa kan irin albashin da wasu jami'an gwamnati ke karba musamman 'yan majalisun tarayya.

"Rashin ayyukan yi da talauci na taimakawa bata-gari wajen samun damar jan hankalin matasa domin aikata laifuka," a cewar kwamitin.

Janar Buhari ma....

Daga cikin mutanen da kwamitin ya tattauna da su har da dan takarar jam'iyyar adawa ta CPC Janar Muhammadu Buhari.

"Kalaman da wasu 'yan siyasa suka yi ciki harda Janar Buhari na neman jama'a su kare kuri'unsu, ya samu mummunar fahimta daga wajen mutane, inda suka fahimci hakan tamkar an ce su tada hankali ne.

Amma a zaman da muka yi da shi Janar din da kansa, mun gano cewa shi ma rikicin ya ritsa da shi, inda aka lalata masa dukiyarsa".

Tuni dai Janar Muhammadu Buharin da ma jam'iyyarsa ta CPC suka nesanta kansu da rikicin da ya biyo bayan zaben na 2011.

Kwamitin ya kuma nemi da a gudanar da sauye-sauye a tsarin mulkin kasar, ta yadda zai zamo koda an yi yunkurin tsige shugaban kasa sakamakon yunkurinsa na kawo sauye-sauye, to hakan ba zai yi wu ba sai an kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a tukunna.

A yanzu dai 'yan kasar da dama ciki harda iyalan wadanda fadan ya ritsa da su sun zuba ido domin ganin matakan da gwamnatin za ta dauka bayan gabatar da sakamakon binciken.

Karin bayani