Kwamitin Lemu na rikicin zabe ya mika rahotansa

Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan
Image caption Kwamitin Lemu daya gudanar da bincike kan rikicin daya biyo bayan zabe yace akwai yiwuwar samun juyin juya hali a kasar matukar ba a dauki matakan da suka dace ba

A Najeriya, kwamitin da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kafa bayan rikicin daya biyo bayan zaben kasar ya mika rahotonsa ga gwamnatin kasar.

Kwamitin ya mika rahoton ne bayan daya shafe watanni yana zagaya wasu sassan kasar da aka sami barkewar rikice rikice a lokacin zaben kasar na watan Afrilu, wanda kuma yayi sanadiyyar asarar rayuka da kuma dukiyoyi da dama, abinda kuma ya kara haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan kasar masu banbance banbacen addini da kabila.

Rahotanni sun nuna cewa kwamitin ya shaidawa mahukuntan kasar halin kunci da fargaba dake zukatan 'yan Najeriya sanadiyyar matsalar tsaro data zama tamkar ruwan dare a kasar

Shugaban kwamitin Sheikh Ahmed Lemu ya ce kamata yayi ayi hattara, domin rashin daukar matakai, ka iya haifar da juyin juya hali a Najeriya, kasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afurka.