An fara shariar Umar Faruk Abdulmutallab

Umar Faruk Abdulmutallab
Image caption Umar Faruk Abdulmutallab

An fara shari'ar dan Nigeriar nan, Umar Faruk Abdulmutallab, wanda ake zargi da kokarin fasa bam a cikin wani jirgin saman Amurka a ranar kirsimeti a shekara ta 2009.

Da yake gabatar da bayanansa na farko ga kotun dake zamanta a birnin Detroit, mai gabatar da kara na tarayya ya ce Umar Farouk Abdulmutallab ya kuduri aikata aikin ta'addanci don kashe mutane kusan 300.

Ana dai zargin Umar Abdulmutallab mai shekaru 24 da kokarin tayar da bam din da ya boye a cikin dan kamfansa yayinda jirgin saman Kamfanin Northwest dake makare da jama'a ke karatar Detroit daga Amsterdam.

Umar Faruk Abdulmuttalab ya musanta wannan zargin.