An saki firsunoni dari da hamsi a Burma

burma Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu firsunoni da aka saki a kasar Burma

Masu fafutukar kare hakkin bil-adama sun ce sabuwar gwamnatin da farar hulla ke jagoranci a Burma, sun saki firsunonin siyasa fiye da dari da hamsin, aka sarinsu wadanda suka shafe shekara da shekaru garkame a gidan kaso karkashin mulkin soji.

Wadanda aka sallamar sun hada da Malaman addinin Buddha, da wani dan jarida da kuma wani fitaccen dan Kama mai suna Zarganar.

Shugabar yan adawa ta kasar Burmar, Aung San Suu Kyi, ta bayyana farin cikinta da sallamo wadannan firsunoni.

Tace"Ina yiwa duk wadanda aka sako maraba, kowannensu na da kima, kuma 'yanci ga dan adam abu ne da ba' a iya kimanta shi".

Taron jama'a da 'yan uwan da suka hallara a kofar kurkukun Insein dake Rangoon sun kece da shewa a lokacin da aka fara sakin fursunonin, yayinda wasu kuma suka yi ta tafi.

Sai dai rahotanni na nuna cewa wadanda suka jagoranci zanga-zangar da bata yi nasara ba a shekarar 1988 suna gidan kaso har yanzu.

'Akwai sauran rina a kaba'

Anata bangaren kungiyar kare hakkin dan'adam ta Amnesty international ta ce akwai bukatar gwamnatin Burma ta saki wasu karin fursunonin idan har da gaske take wajen yin garan-bawul.

Jami'in kungiyar Benjamin Zawacki ya shaidawa BBC cewa "Yawan wadanda aka sakin bai kai ya kawo ba, abu ne da za'a yi murnan ya faru, hakika fursunonin kuma za su yi maraba da hakan, da 'yan uwansu, da abokan arziki".

Amma idan aka dubi alkawuran da gwamnatin ta yi na gaggauata yin garonbawul a fannin siyasar kasar fursunoni 120 ko kusan hakan wato kimanin kashi biyar cikin dari na baki daya fursunonin siyasar da ake tsare da su, adadin bai taka kara ya karye ba.

A halin yanzu dai muna maraba da hakan, amma ba mu ji dadi ba kwata-kwata.

Kasashen yamma dai sun jima suna nuna damuwa game da makomar fursunonin siyasa a Burma.

Haka kuma takunkumin da suka sanyawa kasar na cigaba da aiki.