Kasar Burma ta saki wasu fursunoni

Majalisar dokokin kasar Burma
Image caption Kasar Burma ta saki wasu fursunoni daga gidajen yari karkashin shirin yin afuwa ga fursunoni a kasar

Hukumomi a kasar Burma sun saki wasu fursunoni da aka tsare saboda dalilai na siyasa da suka hada da Shin Gambira, wanda ya taka muhimmiyar rawa a jerin gwanon da gwamnatin kasar ta murkushe a shekarar 2007.

Daga cikin fursunonin da aka sake su har da fitaccen dan wasan kwaikayon nan kuma dan tawaye Zarganar wanda aka kama a shekarar 2008, bayan da ya fito fili ya soki gwamnatin sojin kasar da jan kafa wajen daukar matakai akan mummunar iskar nan ta Nargis, wacce ta halaka fiye da mutane dubu dari da arba'in a kasar.

Wakilin BBC ya ce gwamnatin kasar ta yi alkawarin cewa fiye da fursunoni dubu shida ne dai aka shirya sakinsu a karkashin shirin yin afuwa ga fursunoni a Burma.

Burma dai na yin hakan ne domin burin ta na shugabantar kungiyar kasashen ASEAN. Tana kuma son kasashen duniya su rika girmama ta