Dan bindiga ya harbe mutane takwas har lahira a Carlifornia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'yan sanda na bincike

Mutane takwas sun mutu mutu sanadiyar harbin kan mai uwa da wabi da wani dan bindiga ya kai a wani shagon gyaran gashi a jihar California dake kasar Amurka.

Mutum na tara dai ya jikkata matuka kuma yana aisbiti ne. Wannan lamari dai ya auku ne a garin Seal Beach.

An dai a fara jin karar harbe-harben bindiga ne a lokacin cin abincin rana a wani shagon gyaran gashi da yawanci ke ciki da mutane. Wadanda su ka gani da ido sun ce wani dan bindiga ne ya bude wuta kuma ke harbin kan mai uwa da wabi.

Jami'in tsaron dai sun iso wurin ne a lokacin da aka gama ta'asar idan suka ga gawawaki a kasa sannan wasu sun buya saboda fargabar rayuwarsu.

An dai kama wanda ake zargin da kai harin bayan wani ya ce ya ganshi a lokacin da yake tserewa a cikin mota.

Mutumin dai ya shaidawa 'yan sanda cewa yana dauke da wasu bindigogi ne tare da shi.

Har yanzu dai 'yan sanda sun ce suna bincike domin su gano dalilann daya sa ya kai harin, amma sun se suna kyautata zaton cewa ya kaddamar da harin shi kadai ne.

Harin dai ya sanya al'ummar garin cikin kaduwa, a yayinda garin ya zama garin Amurka na baya-baya nan da ya shiga cikin sahun garuruwan da ake kaddamar da harin bindiga makamancin wannan.