Zargin Amurka kan Iran 'zancen banza ne'-Larijani

Kakakin Majalissar dokokin kasar Iran, Ali Larijani
Image caption Kakakin Majalissar dokokin Iran Ali Larijani

Kakakin Majalissar dokokin kasar Iran, Ali Larijani, yayi watsi da zargin da Amurka ta yi cewar kasar Iran ce da alhakin wani yunkuri na hallaka Jakadan kasar Saudiyya a Amurka, yana

mai cewar wannan zancen banza ne, irin na yara, ko kuma wadanda basu nakalci abun da suke yi ba.

Mista Larijani ya shaidawa majalisar cewar Amurka na son karkatar da hankalin jama'a ne daga matsalolin da ta ke fuskanta a yankin gabas ta tsakiya.

Yace "labarin da muka samu da dumi duminsana cewa Iran a yi watsi da zargin da Amurka ta yi na wata makarkashi ta hallaka jakadan Saudiyya a Washington".

Tun farko dama gidan talbijin na kasar Iran din ya ce gwamnatin Iran ta yi watsi da wannan zargi.

Shi ma jakadan Iran a majalisar dinkin duniya ya ce zargin da Amurka ta ke yi bashi da tushe balle makama.

Yayinda wani mai magana da yawun shugaba Mahmoud Ahmadinajad ya ce Amurka ta saba kirkirar abubuwan da ba gaskiya ba ne.

Kakakin Majalissar dokokin kasar Iran, Ali Larijani, yayi watsi da zargin da Amurka ta yi cewar kasar Iran ce da alhakin wani yunkuri na hallaka Jakadan kasar Saudiyya a Amurka, yana mai cewar

wannan zancen banza ne, irin na yara, ko kuma wadanda basu nakalci abun da suke yi ba.

Mista Larijani ya shaidawa majalisar cewar Amurka na son karkatar da hankalin jama'a ne daga matsalolin da ta ke fuskanta a yankin gabas ta tsakiya.

Yace "labarin da muka samu da dumi duminsana cewa Iran a yi watsi da zargin da Amurka ta yi na wata makarkashi ta hallaka jakadan Saudiyya a Washington".

Tun farko dama gidan talbijin na kasar Iran din ya ce gwamnatin Iran ta yi watsi da wannan zargi.

Shi ma jakadan Iran a majalisar dinkin duniya ya ce zargin da Amurka ta ke yi bashi da tushe balle makama.

Yayinda wani mai magana da yawun shugaba Mahmoud Ahmadinajad ya ce Amurka ta saba kirkirar abubuwan da ba gaskiya ba ne.

'Obama ya yi tur'

Shugaban Amurka Barrack Obama tuni ya yi Allah wadai da Iran kan abinda ya kira keta dokar kasa da kasa.

Haka kuma hukumomi a kasar sun gurfanar da Iraniyawan biyu da ake zargi da kulla makarkashiyar kashe jakadan saudiyya a Amurka ta hanyar amfani da abubuwa masu fashewa.

Atoni janar na Amurka Eric Holder Iran ce ta kulla makarkashiyar tare da daukar nauyi da kuma bada umarni kan yadda za'a aiwatar, saboda haka za su dora al'hakin yunkurin akan gwamnatin Iran.

Ma'aiakatar shari'ar Amurkan dai ta ce rundunar juyinjuya hali ta Iran wato Qods ne suka shirya kisan.

An sha zargin rundunar dai ada kai hare-hare a kasashen waje, amma ba ta taba kaiwa a cikin Amurka ba.

Wasu masu sanya idanu kan al'amura sunce makarkashiyar bata yi kama da aikin rundunar ba, saboda anyi sakaci a yunkurin kisan jakadan kuma abune da za' iya ganowa cikin sauri.

Yayinda wasu sukayi amanna cewa alamu ne dake nuna cewa Iran na yunkurin bin wasu sabbin dabaru na nuna adawa da Amurka.