Ba lallai propopol ne ya kashe Micheal ba

Lauyoyin da ke kare Likitan fitaccen mawakin nan Micheal Jackson sun ce za su janye ikirarin da suka yi cewa mawakin ne ya kashe kansa da kansa.

Tun da farko dai Lauyan likitan ya ce za su gabatar da shaidar cewa Micheal Jackson din ne da kansa ya sha wani maganin rage radadi mai suna propopol da ya wuce kima ba tare da sanin likitan nasa ba.

Sai yanzu lauyan ya ce wani bincike ya nuna cewa shan wannnan magani ba ya wani tasirin a-zo-a-gani.