Rahotanni sun ce an kama Mutassim Gaddafi a Sirte

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutassim Gaddafi ni dai ke baiwa mahaifinsa shawara a kan harkokin tsaron kafin a hambarar da gwamnatinsa

Har yanzu dai ana ci gaba da samu rahotannin da ke karo da juna, kan daya daga cikin yayan Kanal Gaddafi Mutassim, wanda ya yi aiki a matsayin mai baiwa mahaifinsa shawara akan harkokin tsaro.

Wani jami'in gwamnatin Majalisar rikon kwarya a Libya ya ce an kama Mutassim Gaddafi a Sirte, kuma a wuce da shi Benghazi.

Mutane da dama ne dai ke murna bayan sun samu labarin kama Mutassim Gaddafi inda sukai ta harbe-harben bindiga a sama.

Har yanzu Majalisar dai bata nuna wani shaida da ke nuni cewa tana tsare da shi ba.

A baya ma an taba samu rahotannin da ke nuni da cewa an kama wasu daga cikin jami'an Kanal Gaddafi, a yayinda kuma zance ya zama ba haka yake ba.

Wani sojin Majalisar rikon kwarya ya ce dai an kama Mutassim ne a lokacin da ya ke kokarin tserewa daga Sirte a cikin wata 'yar karamar mota.

Amma har yanzu dai a hukumance, Majalisar rikon kwaryar ta ce ba za ta iya tabbatar cewa ko tana tsare da shi ba ko a'a.

Idan dai har ya tabbata cewa an kama Mutassim, zai sama iyalin Gaddafi na farko da sojojin Majalisar rikon kwarya su ka kama a Libyan.

An dai haifi Mutassim Ghaddafi ne a shekarar 1975, kuma yana aikin Likita ne kafin ya shiga soja. Ya dai rike mukamin mai baiwa mahaifinsa shawara kan harkokin tsaro a kasar ta Libya kafin a hambarar da gwamnatin Kanal Gaddafi.

Ana mishi kallon wanda zai iya kalubalantar dan uwanshi Seif al-Islam a matsayin wanda zai gaji mahaifinsu da yana kan mulki.