Amurka na zargin Iran da shirin hallaka jakadan Saudiyya

Shugaban Amurka Barack Obama Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Amurka na zargin kasar Iran da shirin hallaka jakadan kasar Saudi Arabia dake kasar

Hukumomi a kasar Amurka sun sanya takunkumi akan wasu manyan jami'an rundunar juyin juya hali na kasar Iran tare da kira ga kasashen duniya dasu sake mayar da kasar ta Iran saniyar ware.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumomin Amurkan suka ce sun tuhumi wasu 'yan kasar Iran su biyu bisa zargin kulla makarkashiyar hallaka jakadan kasar Saudiya a Washington a wani gidan cin abinci, ta hanyar yin amfani da wasu abubuwa masu fashewa.

Ministan shari'a na Amurka Eric Holder, ya ce kasar Iran ce ta kulla, ta kuma dauki nauyin makarkashiyar yunkurin aiwatar da kisan.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton, ta ce yanzu lokaci ya yi da Amurkan zata aike da sako mai karfi ga kasar Iran tare da kara maida Iran din saniyar ware daga sauran kasashen duniya.

Sai dai a nata bangaren kasar Iran ta musanta cewa tana da hannu, inda ta ce Amurkan na wannan zargin ne saboda ta cimma wata manufa ta siyasa.