Amurka ta zargi Iran da tallafawa ta'addanci

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta bayyana wani makircin kisan Jakadan kasar Saudiyya a kasar Amurka, wanda ake zargin kasar Iran ta kulla a matsayin karuwar hadarin da ke tattare da yadda kasar Irin din ke tallafa wa ta`addanci.

Mrs Clinton ta ce ya kamata a dora wa gwamnatin Iran alhakin lamarin.

Tun da farko dai Ministan harkokin wajen kasar Iran, Ali Akbar Salehi ya gargadi Amurka da ta guji yin fito-na-fito a kan zarge-zargen.

Kasar Amurka dai ta tuhumi wasu `yan kasar Iran Biyu, kana ta sanya takunkumi wa manyan jami`an rundunar juyin-juya-hali ta Iran da kuma wani kamfanin jiragen saman kasar.

Sakatariyar hakokin wajen Amurkan ta ce an taki sa`a jami`an tsaro sun taka-rawar-gani wajen wargaza makircin, kuma makircin karya dokar kasa-da-kasa ne da kuma dokar Amurka.