Babban bankin Jamus ya nuna damuwa

josef Ackermann

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

josef Ackermann

Shugaban daya daga cikin manyan bankuna a duniya, yayi suka akan shirye-shiryen da ake na shawo kan matsalar kudaden da kasashen yankin Euro ke fuskanta.

Josef Ackermann, wanda shine shugaban Deutsche Bank na kasar Jamus, yayi gargadin cewa, al'amurra za su iya tsayawa cik a kasuwannin hada-hadar kudade, saboda yunkurin da ake na tilastawa bankin nasa da sauran bankunan, su dauki karin nauyin asarar da ake samu, sakamakon yadda wasu kasashe irinsu Girka suka kasa biyan basusukan da ke kansu.