Kungiyar dillalan mai ta kasa ta yi barazanar shiga yajin aiki

Kungiyar dillalan man petur ta Najeriya, IPMAN, shiyyar arewa maso yammacin kasar, ta yi barazanar shiga yajin aiki na gama-gari, idan har gwamnatin Najeriya ta nace a kan shirinta, na janye tallafin da take bayarwa a bangaren man petur.

A taron gaggawar da ta yi a Kaduna, IPMAN, shiyyar arewa maso yammar ta ce, ko kadan ba ta amince da aniyar gwamnatin tarayyar ba, na janye tallafin man a farkon shekara mai zuwa.

Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin ke gangamin aiwatar da manufofin tattalin arzikin kasar a wani taro na kwana biyu da ta fara, da nufin kyautata dangantaka tsakanin 'yan kasuwar kasar da kuma gwamnati.

Mahalarta taron, wadanda suka hada da shugaban kasar, da jami`an gwamnati, da kuma manyan 'yan kasuwa sun yini suna tattaunawa a kan ire-iren kalubalen da suke fuskanta, da kuma hanyoyin shawo kansu.

Najeriyar dai na fama da matsalar tabarbarewar tattalin arziki, kasancewar masana'antun kasar da yawa sun durkushe sakamakon karancin makamashi, lamarin da ya haifar da matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa.