An kashe mutane 19 a ci gaba da tashe-tashen hankula a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Masu fafutukar kare hakkin bil Adama sun ce an kashe akalla mutane goma sha tara a ci gaba da tashe-tashen hankula a Syria.

Kungiyar da ke sa ido a kan kare hakkokin bil Adama a Syrian ta ce goma daga cikin mutanen sun mutu ne lokacin da dakarun gwamnati suka kai hari garin Banash dake arewacin kasar yayin da a garin Haara na kudancin kasar 'yan bindiga suka kashe sojojin akalla guda tara.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutanen Syria dubu uku ne suka rasa rayukansu tun bayan da aka fara boren kin jin gwamnati a kasar a watan Maris.

Har wa yau masu fafutuka sun ce ana tsare da dubban 'yan kasar da ke adawa da gwamnati.

Mahukunta a Syria dai sun haramtawa kafafen yadda labarai shiga cikin kasar, abun da kuma yake kamu matsala wajen tantace rahotanni makamacin wannan.