An gurfanar da wasu ministoci ukku a kotu a Uganda

Wasu ministoci ukku na gwamnatin Uganda sun gurfana a gaban kotu a birnin Kampala, domin su kare kansu daga zargin cin hanci da karbar rashawa.

A jiya ne ministocin suka ajiye mukaman su domin su wanke kansu daga zargin - a cewarsu.

Mutanen ukku da suka hada da ministan harkokin wajen kasar ta Uganda, sun musanta cewa sun yi amfani da mukamansu ta hanyar da bata dace ba, dangane da kwantaragin gyara wani hotel

a shekara ta dubu biyu da bakwai, yayin da ake shirin taron kolin Commonwealth a Ugandar.