Taron ministocin kudi a birnin Paris

Wakilai daga kasashe mafiya karfin tattalin arziki suna can suna taruwa a birnin Paris na Faransa, inda za su fuskanci tabarbarewar tattalin arziki da kuma matsalar bashin da ke addabar kasashen Turai, wadanda ke barazanar bazuwa zuwa waje da nahiyar.

Wani jami'i a Faransa ya bayyana yankin da ake amfani da kudin Euro a matsayin cibiyar matsalar kudaden duniya.

Babban Magatakardan Kungiyar Hadin kan Tattalin Arziki da Cigaba, Miguel Angle Gurria, ya ce taron yana da muhimmanci, saboda ministocin kudin ne ke tsara wa shugabanni abubuwan da za su tattauna a kai.