Dakarun Kenya na shirin shiga Somaliya

Kasar Kenya ta ce a shirye dakarunta suke su tsallaka kan iyaka zuwa cikin Somaliya, domin farautar wadanda suka sace wasu baki 'yan kasashen waje.

Ministan tsaron cikin gida na kasar Kenya, George Saitoti ya ce sojojin zasu bi, su zakulo 'yan kungiyar al-Shabaab duk inda suke.

Ya ce, a yanzu sun rufe kan iyakar Somaliya, kuma ba sa nadamar daukar matakin .

Ranar Alhamis da ta wuce ne, aka sace wasu ma'aikatan agaji 'yan kasar Spain su biyu, a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab.

Al-Shabaab dai ta musanta hannu a sace mutanen.

An yi imanin cewa wasu matan biyu 'yan kasashen waje da aka sace a kusa da garin gabar teku na Lamu, an kai su kasar ta Somaliya ne.