Zanga zangar adawa da manyan kamfanoni

Zanga zanga Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zanga zanga

A sassa daban daban na duniya an gudanar da zanga zanga ta nuna adawa da abinda ake yi wa kallon babakeren da manyan kampanoni ke yi.

Zanga zangar da wasu masu fafutuka 'yan tsiraru suka soma a birnin New York, a yanzu ta zama ruwan dare gama duniya.

Dubban jama'a sun taru a biranen Auckland na New Zealand da Sydney na Australia, domin kokawa da yadda tattalin arzikin duniya ya kasance a hannun wasu mutane kalilan kawai.

Haka ma an gudanar da irin wannan zanga zangar a birnin Hong Kong da na Taipei.

A nahiyar Turai ma duk kanwar ja ce - an yi zanga zangar a kasashe irinsu Jamus da Birtaniya da Girka da Spain da Italiya da dai sauransu.

A birnin Rome 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga zangar da su ka fasa tagogin banki da na kantuna, tare da kona motoci.

Zanga zangar na cigaba da bazuwa a ko'ina a duniya, albarkacin hanyoyin sada zumunta na intanet.

Kuma alama ce ta irin matsalar tattalin arzikin da ke cigaba da addabar jama'a.