An tsaurara tsaro a Tripoli

Tripoli Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tripoli

Dakarun sabuwar gwamnatin Libya sun kara tsaurara tsaro a Turabulus, babban birnin kasar, kwana guda bayan wata arangama da wasu magoya bayan hambararren shugaban kasar Kanar Gaddafi.

Gwamnatin rikon kwaryar ta NTC ta kafa wasu karin wuraren binciken ababen hawa, ta kuma gudanar da binciken gida gida a unguwar Abu Salim, inda aka yi musayar harbe harben a ranar Juma'a.

Wannan shi ne karon farko da aka samu barkewar tashin hankali a birnin na Turabulus - ko Tripoli - tun bayan da dakarun dake adawa da Gaddafi suka kwace iko da shi cikin watan Agusta.