Mutane 4 sun hallaka a harin bam a Gombe

Taswirar Najeriya
Bayanan hoto,

Taswirar Najeriya

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane hudu, a wani harin bama-bamai a kan hedkwatar 'yan sandan kwantar da tarzoma dake Gombe.

Hukumomin sun kuma bayyana cewa, harin ya yi sanadiyar kona motoci guda goma sha hudu, da kuma lalata ginin hedkwatar.

Kawo yanzu dai ba a san ko su wanene suka kai harin ba.

Amma hukumomin tsaro sun yi imanin wasu ne masu bukatar kwaso makamai domin aikata miyagun laifufuka.

Tashin bama-bamai a Najeriya na dada yawaita, duk da matakan da jami'an tsaro ke cewa su na dauka.