Shirin musayar fursuna tsakanin Isra'ila da Falasdinawa

Murnar sakin fursunoni Falasdinawa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Murnar sakin fursunoni Falasdinawa

Isra'ila ta fara shirin mika wasu fursunoni Palasdinawa su kusan 500, a matsayin musaya da sojan Isra'ilar nan Gilad Shalit.

Wasu Palasdinawa 'yan bindiga ne suka yi awon gaba da shi a Gaza, a 2006.

Ana tattara fursunonin a wasu gidajen kurkuku biyu, kamin ahuwa da sakin da za a yi masu a ranar Talata mai zuwa.

Fiye da rabin 'yan kason suna zaman daurin rai da rai ne.

Nan da karshen wannan shekarar kuma ake sa ran Isra'ilar za ta saki wasu fursunonin Falasdinawa 550.

A daren jiya, wasu masu gwagwarmaya 'yan tsiraru, sun hallara a gaban gidan shugaban Isra'ilan, Shimon Peres, domin nuna adawa da musayar fursunan.

Ra'ayin jama'ar da wani gidan talabijin ya nema ya nuna cewa, Isra'ilawa masu goyon bayan yarjajeniyar musayar fursunan suna da rinjaye sosai.

A nasu bangaren, iyalan 'yan kason da za a saki, suna ta bayyana farincikinsu.

Dayawa daga cikin fursunonin da za a sakin dai, wadanda aka yankewa jerin hukuncin daurin rai da rai, ba za su iya komawa gidajensu a gabar yammacin kogin Jordan ba.

A maimakon haka za a kai su ne yankin zirin Gaza, ko kuma kasashen waje.