Winston Tubman zai shiga zagaye na biyu na zabe

Taswirar Liberia
Image caption Taswirar Liberia

Mutumin da ya zo na biyu a zaben shugaban kasar Liberia, Winston Tubman, ya shaidawa BBC cewa, zai shiga zagaye na biyu na zaben, domin fafatawa da shugaba mai ci, Ellen Johnson-Sirleaf.

A jiya, Asabar, manyan jam'iyyun adawar Liberiyar, ciki har da ta Mr Tubman, sun yi zargin an tafka magudi a zagayen farko na zaben, suna kira ga magoya bayansu da su yi zanga zanga. Sakamakon da aka fara samu na nuna cewa Mrs Sirleaf ce ke kan gaba da kadan --amma kuma ba ta samu isassun kuri'un da ake bukata ba, domin kauce wa zuwa zagaye na biyu.

Tuni dai ta amince a je zagaye na biyu na zaben.