Karshen farmakin soja a Libiya

Taswirar Libya Hakkin mallakar hoto MAP
Image caption Taswirar Libya

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen haramcin zirga zirgar jiragen saman da ya sanya wa Libya, da kuma shawarar da ta kai ga daukar matakan soji a kasar.

Shawarar da Majalisar Dinkin Duniyar ta yanke domin kawo karshen ayyukan da kungiyar tsaron NATO ke gudanarwa na kai hare hare ta sama a Libya, na faruwa ne a sakamakon rugujewar gwamnatin Gaddafi.

Sai dai sabuwar gwamnatin wucin gadi ta Libyar, ta so NATOn ta ci gaba ad ayyukanta har karshen shekara.

Kudirin dakatar da matakan sojin a Libya zai fara aiki ne mintuna kadan kafin tsakar daren litinin mai zuwa.