Makiyaya sun ajiye makamai a jamhuriyar Nijar

Hakkin mallakar hoto bbc

A jamhuriyar Nijar, wasu makiyaya na yankin arewacin gundumar Walam, kusa da kan iyaka da kasar Mali wadanda ke rike da makamai ba bisa ka'ida ba, sun amince su mikawa gwamnatin kasar makaman.

A ranar asabar ne firayim ministan kasar ta Nijar malam Briji Rafini ya jagoranci bikin karbar makaman a garin na Walam wanda ke da nisan kilomita 98 a arewacin Yamai, babban birnin kasar.

Hakan ya biyo bayan wata yarjejeniya da kasashen Nijar da Mali suka cimma ne a kwanakin baya.

Fulanin dai sun ce sun dau makaman ne domin kare kansu da dukiyoyinsu daga hare-haren da wasu mutane dauke da makamai wadanda ke fitowa daga kasar ta Mali ke kai musu.