Alaa da Gamal na da makudan kudade a Swiss

Wani babban jami'i a ma'aikatar shara'ar Misra, Assem Al-Gohari yace 'yayan tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak, wato Alaa da Gamal, nada tsabar kudi kimamin dalar Amurka miliyan dari-ukku-da-arbain a bankunan Swirztland.

Al-Gohari yace yawancin kudin na babban dan Mubarak ne wato Alaa, kuma yanzu haka hukumomin kasar Swirdland na gudanar da bincike akan Alaa din a bisa zargin halalta kudin haram.

Alaa da Gamal dama mahaifinsu na fuskantar sharar'a a Misra a bisa zargin cin hanci da rashawa.